Austreliya ta ce ta sami rahotannin kungiyar leken asiri da ke nuna cewa `yan ta’adda na shirin kai mata hari a cikin kasar.
November 2, 20052. Austreliya ta ce ta sami rahotannin kungiyar leken asiri da ke nuna cewa `yan ta’adda na shirin kai mata hari a cikin kasar.
Firamiyan kasar Austrreliya, John Howard, ya ce jami’an tsaron kasar sun sami rahotannin leken asirin da ke nuna cewa, ana shirn kai wa kasarsa harin `yan ta’adda. Firamiyan ya bayyana hakan ne a wani taron maneman labarai a birnin Canberra, amma bai ba da karin bayani kan rahoton barazanar harin ba, wanda ya ce a cikin wannan makon ne jami’an tsaron suka samu.
Sanarwar John Howard din dai ta zo ne a daidai lokacin da gwamnatinsa ke kokarin gabatad da wata dokar yaki da ta’addanci ga majalisar kasar, wadda kuma take son ganin an zartar kafin kirismeti. Kawo yanzu dai, ba a taba kai wani mummunan hari a cikin Austreliya din ba. Amma an sha afka wa `yan kasar da kuma ofisoshin diplomasiyyarta a ketare, da harin bamabamai, musamman ma dai a kwanakin bayan nan a kasar Indonesiya.