1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Australia ta sanya hannu kan yarjejeniyar Kyato

Ibrahim SaniDecember 3, 2007
https://p.dw.com/p/CVvv

Faraministan Australia Kevin Rudd ya sanya hannun amincewa da yarjejeniyar yaƙi da ɗumamar yanayi ta birnin Kyoto. Matakin ya kasance aikinsa na farko ne jin kaɗan da rantsar da shi, a matsayin sabon Faraministan ƙasar. Rantsuwar ta zo ne kwanaki tara da lashe zaɓen ƙasar daya kawo ƙarshen mulkin shekaru 11 na Faraminista John Howard. Batun yaƙi da ɗumamar yanayi da kuma inganta harkokin tattalin arziƙin ƙasar na daga cikin manya-manyan ayyukan da sabon Faraministan ya sako a gaba. Har ila yau shugaban ya sanar da shirin janye dakarun sojinta ƙasar daga Iraƙi.