Australia ta sanarda haramtawa jiragen Koriya ta arewa shiga tashoshinta | Labarai | DW | 16.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Australia ta sanarda haramtawa jiragen Koriya ta arewa shiga tashoshinta

Maaikatar harkokin wajen kasar Australia ta sanarda haramtawa manyan jiragen ruwan Koriya ta arewa shiga tashoshinta,a ciga da kara tsaurara takunkumi akan Koriya ta arewan,sakamakon gwajin makamin nukiliya da tayi.

Kasar Australia wace babbar kawace ta Amurka tana goyon bayan kafa tsatsauran takunkumi akan Koriya ta arewa hakazalika ta bada goyon bayanta ga kudirin komitin sulhu na majalisar dinkin duniya daya lakabawa Koriyan takunkumi.

Ministan harkokin wajen Australia Alexander Downer yace sun kara wannan takunkumi ne bisa wadanda komitin sulhun ya kafawa Koriyan ne saboda kara jaddada goyon bayansu ga kudirin komitin suhlu na majalisar dinkin duniya.