Australia ta rufe ofishin jakadancinta a Ramallah | Labarai | DW | 07.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Australia ta rufe ofishin jakadancinta a Ramallah

Gwamnatin kasar Australia tace ta rufe ofishinta na jakadanci na wucin gadi,a yankunan palasdinwa, ta kuma gargadi yan kasarta da suyi taka tsan tsan game da tafiye tafiye zuwa kasashen Israila,Lebanon Syria da kuma Iran,saboda tashe tashen hankula da suka barke biyowa bayan zanen manzon Allah(SAW) cikin wasu jaridun kasashen turai.

Ministan harkoin wajen Australia Alexandert Downer ya fadawa majalisar dokokin kasar cewa,an rufe ofishin jakadancin ne a Ramalla saboda yana makwabtaka da ofishin jakadancin kasar Denmark da masu zanga zanga suke ci gaba da kai masa farmaki sakamakon wadannan zane zane da suka batawa musulmin duniya rai.