Aung San Suu Kyi ta cika shekaru 61 | Labarai | DW | 19.06.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Aung San Suu Kyi ta cika shekaru 61

A yau ne sananniyar mai gwargwarmayar Democradiyyan nan ta Myammar Aung San Suu Kyi,ta gudanar da bukin cika shekaru 61,a yayinda take cigaba da kasancewa cikin daurin talala a gidanta,ayayinda a hannu guda kuma masu fafutukan demacradiyya ke gudanar da gangami akan mulkin kama karya na soji.

Ana saran yau din dai zaa gudanar da gangami a kasashe sama da 25 dake nahiyoyin Asia da turai da arewacin Amurka ,domin bukatar sakin wannan baiwar Allah,San Suu kyi,wadda ta kasha shekaru 10 daga cikin 17 da suka gabata cikin daurin talala,saboda fafutukan taw a democradiyya.

To sai dai bias dukkan alamu,wannan yukuri nasu bazai cimma tudun dafawa ba a garin na Yangon,inda sojojin dake mulkin tsohuwar janhuriyar Barma ,tun daga shekara ta 1962,ta tsananta matakan tsaro a titunan dake zuwa gidan San Suu Kyi ,da kewaye.

A ranar 27 ga watan mayun daya gabata nedai aka dada fadada waadin daurin talala da ake mata ,da Karin shekara guda,duk da matsin lanba da kashen duniya keyi,da kuma kiran kai tsaye da sakatare general na mdd Kofi Annan yayi wa shugaban mulkin sojin Than Shwe,na bukataer sakinta.

 • Kwanan wata 19.06.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu6a
 • Kwanan wata 19.06.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu6a