Aung San Suu Kyi- Ba za ta halarci taron MDD ba | Labarai | DW | 13.09.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Aung San Suu Kyi- Ba za ta halarci taron MDD ba

Shugabar kasar Myanmar Aung San Suu Kyi, ta yi watsi da babban taron Majalisar Dinkin Duniya da zai gudana a birnin New York na Amirka. Mai magana da yawun shugabar ne ya bayyana niyar shugabar a gabannin taron.

Myanmar - Aung San Suu Kyi (Reuters/E. Su)

Shugabar kasar Myanmar, Aung San Suu Kyi

Ana danganta matakin kauracewa taron ba ya rasa nasaba da matsin lamba da shugabar ke fuskanta daga bangarori da dama, kan rashin kawo karshen rikicin kabilanci da ya ritsa da musulmai 'yan kabilar Rohingya. Rikicin da ya barke a watan Agusta, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama, yayin da akalla mutane dubu 370,000 ke gudun neman tsira a kasar Bangaladesh kamar yadda hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta nunar watau UNCHR.