Aukuwar harin ƙunar bakin wake a Turkiya | Labarai | DW | 31.10.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Aukuwar harin ƙunar bakin wake a Turkiya

Mutane 15 sun rasa rayukansu a cikin wani hari da aka aiwatar a Turkiya.

default

'Yan sanda Istanbul da ke bincike akan harin ƙunar baƙin wake.

Mutane aƙalla guda 32 suka samu raunuka bayan da wani abu ya yi bindiga ya kuma fashe a tsakiyar cibiyar hada-hadar kasuwanci ta Taxim da ke Istanbul babban birnin kasar Turkiya. Fashewar bam ɗin wanda shugaban hukumar 'yan sanda na birnin, Huseyin Capkin ya ce suna kyautata zaton cewa harin ƙunar baƙin wake ne, ya zuwa yanzu ba a san ko wanda ya yi dalilinsa ya mutu a ciki ba. Kuma har yanzu ba a da masaniya dangane da wanda suka ɗauki alhakin kai harin da a cikinsa 'yan sanda guda shidda da fararen fula tara suka jikata .

Mawallafi: Abdourahamane Hassane

Edita: Halima Balaraba Abbas