1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AU ta yi Allah wadai da yunƙunrin juyin mulki a ƙasar Tchad

March 16, 2006
https://p.dw.com/p/Bv4r

Ƙungiyar taraya Afrika, ta yi Allah Wadai da yunƙurin juyin mulki da wasu sojoji su ka shiraya a ƙasar Tchad a ranar talata da ta gabata.

Sakataran zartaswa na wannan ƙungiya Alfa Umar Konare, ya jaddada matsayin AU, na haramta juyin mulki a matsayin kafar hawa kan kagarar mulki.

Konare ya yi kira, ga sassa daban-daban na siyasa a ƙasar su hau tebrin shawarwari, domin magance matsalolin siyasa da ƙasar ke fuskanta.

Idan dai ba a manta ba, jiya ne, gwamnatin Tchad, ta hiddo sanarwar murƙushe wani juyin mulki, da yan tawaye su ka buƙaci aikatawa, tare da goyan bayan wasu sojoji masu biyyaya ga gwamnati.

Kakakin gwamnatin ƙasar Tchad ya ce, an kama 2 daga sojojin da aka samu, da hannu a cikin yunƙurin juyin mulkin.

Hukumomi Tchad, na zargin Sudan da cinna wutar rikici da ke shirin kamawa, a wannan ƙasa.