AU ta yi Allah wadai da take haƙƙoƙin jama´a a Zimbabwe | Labarai | DW | 17.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

AU ta yi Allah wadai da take haƙƙoƙin jama´a a Zimbabwe

Hukumar zartaswa ta ƙungiyar taraya Afrika, ta bayyana sanarwar Allah wadai, ga abubuwan da su ka wakana a ƙasar Zimbabwe a makonda mu ke ciki.

Idan dai ba a manta ba, jami´an tsaro ,sun yi duka mai tsanani, ga madugun yan adawa Morgan Tchagirai, tare da sauran mutane fiye da 50, a yayin da su ka shirya wata zanga-zangar lumana.

Shugaban hukumar zartaswa ta AU Alpha Omar Konare, ya ce ko kussa, bai dace ba , cin zarafin da ya wakana a ƙasar Zimbabwe, sannan yayi kira ga ɓangarorin 2, su koma tebrin shawara, domin samnar da mattakan warware rikicin siyasar kasar cikin lumana.

Ƙungiyar taraya Afrika, ta buƙaci shugaba Robert Mugabe, ya umurci jami´an tsaro, su kiyaye haƙƙoƙin bani adama, da kuma tabbatar da yancin faɗin albarkacin baki, daidai da yadda dokokin ƙungiyar ta haɗin kann Afrika su ka tanada a dukkan ƙasashe membobin ta.