1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AU ta tura wakili a NDjamena da zumar samar da fahintar juna tsakanin Tchad da Sudan

Yahouza SadissouApril 17, 2006

Ƙungiyat Tarayya Afrika ta aika wakili a ƙasar Tchad, bayan sanarwar da Idriss Deby Itno yayi ta katse hulɗoɗin diplomatia da Sudan

https://p.dw.com/p/Bu0a
Hoto: AP

A yammacin jiya ne, shugaban komitin zartawa na ƙungiyar tarayya Afrika, Alfa Omar konrre ya tura wakili na mussaman a ƙasar Tchad, domin tantanawa da shugaban Idriss Deby Itno, a game da halin da a ke ciki, a rikici, tsakanin Tchad da Sudan, bayan artabon da a ka yi amakonda ya gabata tsakanin rundunoninTawaye da na gwamnatin Tchad.

Idan dai ba a manta ba, ranar juma´a da ta wuce, shugaban ƙasar Tchad, ya bayyana katse hulɗoɗin diplomatia da Sudan, a sakamakon zargin da yayi wa gwamnati Khartum, na kunna wutar rikicin tawaye a Tchad.

Sannan ranar lahadin shekaran jiya, tawagar Tchad, ta fita daga zauran taron sulhunta rikicin yankin Darfur, da ke ci gaba da gudana a birnin Abuja na Tarayya Nigeria.

Nan gaba a yau ne, wakilin na Kungiyar tarayya Afrika Ambassada Abdulkader Ture, zai haɗu da shugaban ƙasar Tchad, domin gabatar masa da jawabin da ya ke ɗauke da shi.

Wannan ziyara, ta biwo bayan wata makamanciyar ta, da ministan kulla da harakokin Afrika, na gwamatin Lybia ya kai a birnin N´Djamena.

Ali Abdessalam shima, ya gana da shugaba Idrissd Deby a dangane da rikici tsakanin Tchad da Sudan..

A watan Februaru na wannan shekara, ƙasar Lybia ta jagoranci wani taro, wanda a sakamakon sa aka samar da sulhu tsakaninTchad da Sudan.

To saidai harin da yan tawaye su ka abkawa birnin N Djamena, a makon da ya gabata, ya maida ciwo ɗanye.

A wata hira da yayi da manema labarai, ministan harakokin wajen Tchad, Ahmat Allami ,ya bayyana cewar, bayan gagaramar nasara, da su ka samu, ta fattatakar yan tawaye, Sudan, ta fara shirya wata sabuwar runduna, da zata kai sabin hare-hare ga ƙasar Tchad.

A nasu ɓangare hukumomin Sudan sun mussanta wannan zargi.