ASUSUN TAIMAKON LIBERIA | Siyasa | DW | 09.02.2004
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

ASUSUN TAIMAKON LIBERIA

Kasahe masu arzikin masana'antu sun yi alkawarin baiwa kasar Liberia taimako kudaden da suka tasama dola miliyan 520,ko hakan ya taimaka wajen sake gina wanan kasa ta yammacin Africa da yakin basasar shekaru goma sha hudu ya dai daita,baya kuma ga mastsaloli na karbar rashawa da almubaranci da halin yanzu zama ruwan dare gama duniya a tsakanin jami'an gwamnatin ta Liberia. Shi kuwa Mark Malloch Brown shugaban hukumar raya kasahe ta majalisar dikin duniya,da suka dauki nauyin gudanar da baban taron asusun taimakawa Liberia na kwanaki biyu ,ya baiyana cewa kasahe masu arzikin masana'antu yi alkawarin baiwa kasar Liberia taimako har na fiye da dola miliyan 500 da za'a yi amfanin da su wajen sake gina Liberia. Tun ranar juma'ar data gabata ne dai wakilan kasahe da suka halarci baban taron asusun taimakawa Liberia,suka yi alkawarin bada taimakon kudade da suka tasama dola miliyan 488. Wanan taro dai na asusun taimakawa Liberia,Amurka majalisar dikin duniya da kuma bankin duniya ne suka dauki nauyin gudanar da shi,wanda kuma ya sami halartar wakilai daga kasahe 90 na duniya da kuma kungiyoyin bada agaji masu zaman kann su da suka kai 40,abin kuma da ake ganin ba'a tama samu irinsa ba a wanan karamar kasa ta yammacin Africa mai yawan aluma miliyan uku da dubu dari uku. A nasa jawabin baban sakatare janar na majalisar dikin duniya Kofi Anan,ya nuna fargabar cewa matukar ba daukar matakan da suka dace aka yi ba na kawo karshen rikici rikicin dake faruwa a Liberia aka yi ba cikin hanzari,to kuwa na iya yaduwa izuwa makwabtan kasahe. Shi kuwa sakataren harkokin wajen Amurka Colin Powell,cewa yayi Amurka ta yi alkawarin baiwa Liberia agaji na dola miliyan 200,tare kuma da yin kira ga kasahen duniya da su taimaka wajen ganin an ceto rayuwar kanan yaran Liberia da aka tilastawa shiga aiyukan soji,ko kuma cin zarafin su ta fanoni da dama. Colin Powell din dai ya kara da cewa zasu dauki matakan tabatar da ganin,kanan yaran Liberia sun fara daukar litatafan su zuwa makaranta,amman ba daukar bindiga kirar Ak-47 ba. Da cikin wanda suka baiwa kasar ta Liberia yi alkawarin baiwa Liberia taimako mai tsoka har da kasahen turia da suka yi alkawain bada taimakon dola miliyan 250,sai kuma bankin duniya da ya ce shima zai bada talafin dola miliyan 50. Duka dai wadanan kudade da aka samu a matsayin taimako ga Liberia,za'a yi amfanin da su ne wajen samar da kayayakin more rayuwa da suka hadar da tsabtace birnin Monrovia,ingantar harkar sufuri da kuma sadarwa a wanan kasa ta yammacin Africa. Shugaban gwamnatin Rikon kwaryar Liberia Gyude Bryant,yayi alkawarin cewa zai tabatar da ganin an kashe wadanan kudade na taimako ta hanyoyin da suka dace,inda yace gwamnatinsa zata bulo da matakan yaki da karbar rashawa da ya adabi wanan kasa. Wani jami'in majalisar dikin duniya dake Liberia.ya baiyana cewa fiye da alumar Liberia 250,000 suka rasa rayukan su,yayin da wasu 500,000 suka rasa matsugunan su na asali,yayin kuma da wasu yan Liberia 250,000 suka yi gudun hijira zuwa wasu kasahe tun lokacin yakin basasa ya barke a Liberia cikin shekara ta 1989. Tuni dai Colin Powell da kuma wasu jami'an diplomaciya na duniya suka bukaci,kwamitin sulhu na majalisar dikin duniya ya dauki matakan kwace dukanin kadarorin Charles Taylor da kuma iyalansa,tun bayan da aka zarge shi da laifin amfani da kudaden gwamnati wajen taimakon aiyuka na yan tawaye a makwabiyar kasar Saliyo.
 • Kwanan wata 09.02.2004
 • Mawallafi JAMILU SANI
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvm0
 • Kwanan wata 09.02.2004
 • Mawallafi JAMILU SANI
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvm0