Assusun bada lamani na dunia zai zaɓi saban shugaba | Labarai | DW | 28.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Assusun bada lamani na dunia zai zaɓi saban shugaba

Nan gaba a yau ne, assusun bada lamani na dunia zai zaɓi saban shugaba, wanda zai cenji shugaba mai ci yanzu Rodrigo Rato, ɗan ƙasar Spain, wanda ya yi murabus daga wannan muƙami.

Zaɓen zai wakana tsakanin yan takara guda 2, wato Dominique Stauss-Khan, na ƙasar France dake matsayin ɗan takara ƙungiyar gamaya turai, da kuma Joseph Tosovosky tsofan Praministan ƙasar Tchecoslovaquia, wanda ya samu goyan bayan ƙasar Russia.

Idan ba wani iko ba daga Allah, alamomi sun nunar da cewa Dominique Strauss Khan zai lashe wannan zaɓe, ta la´akari da goyan bayan da ya samu, daga ƙasashen turai da Amurika, da kuma ƙasashe da dama na yankin Latine Amurika, kamar Brazil da Argentina.

DSK mai shekaru 58 a dunia, ya riƙe matsayin ministan kuɗi na France, kazalika,ya na ɗaya daga shugabanin jam´iyar yan gurguzu ta ƙasar, wada a cikin ta, ya shiga takara zaman shugaba ƙasa, amma Segolene Royal ta taka masa birki.