1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Assad: Trump na iya zama abokin hulda

November 16, 2016

Shugaban Siriya Bashar al Assad yace shugaban Amirka mai jiran gado Donald Trump na iya zama abokin hulda wajen yaki da ta’addanci.

https://p.dw.com/p/2SlGt
Syrien Präsident Bashar al-Assad
Hoto: Reuters/SANA

A kalamansa na farko da ya yi kan sakamakon zaben Amirka, Assad ya shaidawa wata tashar Talabijin ta kasar Portugal cewa za su sa ido su gani ko Donald Trump zai sauya manufar Washington a kann Siriya. Assad yace shugaban dan Republican ya yi wasu alkawura masu armashi akan yakin da ke gudana  amma shin zai iya cika wa? Trump dai ya sanya ayar tambaya akan hikimar Amirka na mara wa yan tawaye baya, ya kuma sassauta batu kan burin Amirka na kawar da Assad daga karagar mulki, yana mai cewa ko da yake baya kaunar sa, Assad na kashe yan IS tare da taimakon Iran da kuma Rasha.Trump ya nuna cewa ba zai matsawa gwamnatin Assad ba a manufofinsa na ketare, yana mai cewa yaki day an IS ya fi muhimmanci a gare shi maimakon yaki da gwamnatin Siriya.