1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Aski ya kai gaban goshi a taron kolin kungiyar ciniki ta duniya

December 17, 2005
https://p.dw.com/p/BvG6

Kungiyar cinikaiya ta duniya WTO zata soke dukkan tallafin da ake ba wa kayan albarkatun gona da ake fitarwa zuwa ketare. Hakan dai na kunshe a cikin daftarin sanarwar bayan taron kolin da kungiyar ke yi a Hongkong. Hakazalika kungiyar ta yi wani tanadin taimako na musamman ga kasashe matalauta. Mahalarta taron su kimanin 149 zasu ci-gaba da tattaunawa akan daftarin sanarwar bayan taron har zuwa gobe lahadi. A yau ma dai an fuskanci mummunar zanga-zanga ta masu adawa da hadakar manufofin cinikaiya na duniya a gaban zauren taron. Musamman manoman kasar KTK dauke da sanduna sun yi arangama da ´yan sandan kwantar da tarzoma.