1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ashton na ziyarar Gabas ta Tsakiya

Ashton zata gana da shugaba Mahmud Abbas a yau Asabar, kana a gobe ta ziyarci zirin Gaza

default

Catherine Ashton

Babbar jami'ar harakokin diplomasiyar ƙungiyar Tarayyara Turai Catherine Ashaton ta fara ziyarar kwanaki ukku a yankin Gabas ta Tsakiya ciki kuwa har da kai ziyara yankin zirin Gaza da Isra´ila ta killace.

A lokacin wannan ziyara ana fatan Ashton  zata gana da shugaba Mahmud Abbas a yau Asabar, kana a gobe ta ziyarci zirin Gaza. Wannan dai ita ce ziyarar ta farko a yankin tun bayan harin da sojojin Isra´ila suka kai akan ayarin jiragen ruwan kayan agajin ga Palaɗinawan Gaza da ya kashe mutane tara, harin da kuma ya jawo wa Isra´ilan tofin Allah tsine daga ƙasashen duniya da dama.

A wata sanarwa da ta fitar, Ashton ta ce ƙungiyar EU ta shirya gabatar da wani ƙudiri da zai samar da mafita game da takunkumin da Isra´ila ta ƙaƙabawa yankin na Gaza wanda ke ƙarƙashin mulkin gwamnatin Hamas mai kishin addinin Islama.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Yahouza Sadissou Madobi