1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ASEAN: An gargadi Koriya ta Arewa kan kera makamin nukiliya

Ramatu Garba Baba
March 18, 2018

Kasashen gabashin Asiya sun gargadi Koriya ta Arewa kan shirin ta na kera makaman nukiliya inda suka nemi Majalisar Dinkin Duniya da ta dauki matakin sanya wa kasar takunkumi in har ta ki sauraron wannan kira.

https://p.dw.com/p/2uXLk
Gruppenfoto Asean-Gipfel 2018
Hoto: picture alliance/AAP/dpa/D. Himbrechts

Shugabanin yankin wato ASEAN sun yi wannan jan kunnen ne a yayin da suka soma zaman taron da suke yi duk shekara shekara. Sun nuna damuwa kan matakin da Koriya ta Arewa ta dauka na ba gudu ba ja da baya a batun kera da kuma gwaje-gwajen makaman nukiliyan duk da barazanar da hakan ke yi ga zaman lafiya a duniya.

Taron ya kuma nemi kasashe da suka kasance mambobi karkashin Majalisar Dinkin Duniya da su sanyawa Koriya ta Arewa takunkumi in har ta yi watsi da wannan kira. Taron kolin na bana na gudana a kasar Australiya inda Firaiministan kasar, Malcolm Turnbull ya kasance mai masaukin baki.