Asalin kafa ƙungiyar Red Cross da Red Cresent | Amsoshin takardunku | DW | 12.08.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Asalin kafa ƙungiyar Red Cross da Red Cresent

An fara kafa ƙungiyar Red Cross ne a shekarar 1863 a birnin Geneva na Switzerland

default

Alamun ƙungiyar Red Cross da Red Crescent

An fara kafa ƙungiyar Red Cross ne a shekarar 1863 a birnin Geneva na Switzerland. Kuma wanda ya kafa ta ana kiran sa Henry Dunat tare da haɗin guiwar wasu mutane huɗu. Kuma tun farko ya kafa ƙungiyar ce domin bada taimakon jin ƙai ga wadanda suka samu kansu cikin wani bala'i ko matsala dake neman agajin gaggawa musanman mai nasaba da wani ciwo. Kawo yanzu dai, a duniya baki-daya, ƙungyiar ta Red Cross, tana da wakilai miliyan 97 dake gudanar da aiyukan  taimako ba tare da samun wani albashi ba.

A shekarar 1919 aka faɗaɗa wannan ƙungfiya ta zama ta ƙasa da ƙasa, kuma yanzu haka tana da rassa 186 da ke aikin taimakon kai da kai, ba dare ba rana domin taimakon al'umma. Sau uku wannan ƙungiya ta Red Cross tana samun kyautar Nobel ta zaman lafiya- wato a shekarar 1917 da 1944 da kuma 1963. Kuma har yanzu, ƙungiyar tana da babban ofishin ta ne a birnin Geneva na Switzerland.

Daga bisani ne dai aka kafa reshen ƙungiyar na Red Cresent domin ƙasashe ko al'umomin da ke yankunan da musulmi suke da yawa, domin dakushe fassarar da akewa ƙungiyar cewar ta mabiya addinin Kirista ce. Daga cikin aiyukan da kungiyar ke gudanarwa sun haɗa da; bada taimakon kai da kai musanman a sha,anin kula da lafiya da kuma jin ƙai ga mabuƙata.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Zainab Mohammed Abubakar