Artabu tsakanin ´yan sanda da masu zanga-zanga a kasar Masar | Labarai | DW | 22.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Artabu tsakanin ´yan sanda da masu zanga-zanga a kasar Masar

Akalla mutane 3 aka kashe sannan kimanin 80 suka jikata a wata arangama da aka yi tsakanin musulmi masu zanga-zanga da ´yan sanda a birnin Alexandria na kasar Masar. Musulmi kimanin dubu 5 suka yi gangami a gaban majami´ar Orthodox ta Optic don gudanar da zanga-zangar yin Allah Wadai da wani faifayen DVD na wani wasan kwaikwayo da al´umar Kiristan yankin suka fitar. Wasan dai na wani kirsta ne dalibi a wata jami´a wanda bayan ya musulunta sai wani babban malami ya tilasta masa kisan fada fada da kuma kone majami´u. Masu zanga-zangar sun bayyana wasan kwaikwayon da cewa tsokana ne kuma ya ci mutuncin addinin Islama.