Armeniya: Za a koma tattaunawa da 'yan adawa
April 24, 2018Talla
Lamarin dai na zuwa biyo bayan zanga-zangar da ta yi awon gaba da kujerar firaminista kasar ta Armeniya. A wani sako da kafafan yada labaran kasar ta Armeniya suka fitar an jiyo mataimakin shugaban majalisa Eduard Sharmazanov na cewa a ranar Laraba ne za a fara tattaunawar. Serzh Sargsyan, wanda ya sauka daga mukamin firemiya a ranar Litinin, a baya ya yi mulki karkashin tsohuwar tarayyar Sobiyat tsawon kimanin shekaru 10 kafin kammala wa'adin mulkin a bana.