1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Aras: Sabuwar kakakin majalisar jiha

Pazarkaya, Utku / Zainab Mohammed AbubakarMay 19, 2016

Kwararriya a fannin tattalin arziki Muhterem Aras ta taka rawa a siyasar Jamus, yanzu ta zame mace musulma ta farko da ta zama kakakin majalisar jihar Baden-Württemberg

https://p.dw.com/p/1Ipow
Stuttgart Landtag Muhterem Aras (Bündnis 90/Die Grünen),
Hoto: picture-alliance/dpa/M.Murat

Ako da yaushe dai Muhterem Aras na cikin kuzari. Babban Fatanta a wannan mukami mafi girma na biyu bayan fraimiyan jihar dai, shi ne kara kimar majalisa tare da karfafa gwarin gwiwa game da harkokin demokradiyyar kamar yadda ta ayyana...

Ta ce "abunda na ke fata kuma keda muhimmnci a gareni shi ne yin mahawara da gabatar da jawabai a tarurruka, ta haka ne za mu iya yin musayar bayanai kan manufofinmu da muhimmancinsu, kazalika da dalilan da yasa muke fafutuka domin cimma ma buri a kansu, tare da nazarin mene ne zai iya kawo hadin kai tsakanin al'umma?"

Aras na muradin yin wannan mahawara da dukkan wakilan bangarori na al'umma. Acewarta hakan zaisa muyi farin ciki dangane da kyawawan manufofin kowane bangare na jama'a. Sai dai ta yi gargadin cewar ba anan kadai zata tsaya ba....

Ta ce "a tsakaninmu komai na tafiya daidai. Nakan yi tunanin cewar, a matsayinmu na al'umma bamu san muhimmamncin da muke da shi ba. Wannan ita ce irin mahawarar da nake muradin in kirkira"

A matsayinta kakakin majalisar jiha, Aras zata shugabanci duk zaman majalisa da za'ayi. Daura da hakan, itace kuma shugabar gudanarwar majalisar dokoki da jami'ai 170 a karkashinta.

Deutschland Wahl des Ministerpräsidenten von Baden-Württemberg
Aras Muhterem da fraimiyan Baden-Württemberg Winfried KretschmannHoto: Reuters/R. Orlowski

Bisa la'akari da inda ta kai a yanzu, ana iya cewar Aras ta yi gagarumin fafutuka kuma kwalliya ta biya kudin sabulu. Mai shekaru 50 da haihuwa, an haifi wannan baiwar Allah ne a wani dan karamin kauye da ke yankin gabashin Turkiyya kuma ta zo Jamus tare da iyayenta ne lokacin da take 'yar shekaru 12.

Tare da tallafin iyayenta ta kasance malamar makaranta kafin ta zama mai bada shawara kan harkokin haraji a birnin Stuttgart kusan shekaru 20, a yanzu haka tana da ma'aikata guda 12 da ke aiki a karkashinta. Mahaifinta ya yi aiki a kusa da birnin Stuttgart a yayin da mahaifiyarta bata yi karatub ba. Sai dai duk da haka iyayenta sun sanya fifiko a kan ilimi. Kana Aras ta yi dace da kasancewarta a nan Jamus. A hannu guda kuma iyayenta sun kasance masu sassaucin ra'ayi na musulunci.