1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Arangama tsakanin sojojin Isra´ila da dakarun Jihadil Islami a Jenine

January 31, 2006
https://p.dw.com/p/Bv9z

Mutane 2 daga bangaren Palestinawa, su ka rasa rayuka a sakamakon wata arangama da aka yi, tsakanin rundunar Israeala da yan yakin sunkuru na kungiyar Jihadil Islami.

Wanan arangama ta wakana a yamacin yau bayan da sojojin Israela su ka yi kutse a garin Arraba na kussa da Jenne.

Mutanen 2 da su ka rasa rayuka sunhada da Nidal Abu Saada shugaban reshen Jihadil Islami, na yankin yamma ga kogin Jordan.

Kakakin rundunar Isra´ila ya nunar da cewa, mutanen 2 ,na da hannu cikin hare haren ta´adanci, da Palestinawa ke kaiwa Isra´ila.

Su na kuma daga mutanen, da su ka kai hare hare 7, na karshe a yankun Isra´ila.