Arangama tsakanin Hamas da Fatah | Labarai | DW | 09.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Arangama tsakanin Hamas da Fatah

An sake fuskantar arangama tsakanin magoya bayan Hamas da kuma Fatah a yankin zirin Gaza a safiyar yau ɗin nan, inda rahotanni suka baiyana cewa wasu matasa magoya bayan Hamas sun buɗe wuta a kan wani ɗan jamíyar Fatah. Yan Fatah ɗin sun mayarda martani tare da musayar wuta. A ranar litinin ɓangarorin biyu sun yi ɗauki ba daɗi wanda ya haddasa mutuwar mutuwar mutane uku, a wani mataki dake nuni da cewa ɓangarorin biyu dake gaba da juna na shirin faɗawa cikin wata gagarumar taƙaddama.