Arangama tsakanin ɗalibai da ´yan sanda a gaban jami´ar Teheran | Labarai | DW | 08.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Arangama tsakanin ɗalibai da ´yan sanda a gaban jami´ar Teheran

Fiye da dalibai 100 sun yi arangama da ´yan sanda da kuma magoya bayan shugaban Iran Mahmud Ahmedi-Nejad a harabar jami´ar birnin Teheran. Dalibai a wajen wani zaure da shugaba Ahmedi-Nejad ya yiwa jawabi sun yi ta ihu suna cewa mutuwa ta kasance kan shugaban mulkin kama karya. Su kuwa dalibai magoya bayan shugaban sun mayar da martani suna masu nuna goyon bayansu ga shugaban dari bisa dari. a lokacin da shugaban na Iran ke jawabi a cikin wani zaure.Wadanda suka shaida abin da ya faru sun ce an kame dalibai da dama masu tarzoma. A cikin watan desamba na shekara ta 2006, wasu dalibai a wata jami´a daban sun yi ta ihu a lokacin da shugaba Ahmedi-Nejad ke jawabi.