Arangama tsakanin ƙungiyoyin ƙwadago da jami´an tsaro a ƙasar Guinee | Labarai | DW | 17.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Arangama tsakanin ƙungiyoyin ƙwadago da jami´an tsaro a ƙasar Guinee

A birnin Conakry na ƙasar Guinee, a na ci gaba da arangama, tsakanin jami´an tsaro da ƙungiyoyin ƙwadago.

A sakamakon taron gangamin da su ka shirya, ƙungiyoyin ƙwadago sun bukaci shugaban ƙasa, Lansana Konte, ya yi murabus daga muƙamin sa.

Shugaban Majalisar Dokoki ya kiri ƙungiyoyin su daina zanga-zanga, tare da alkawarta ƙarin albashi, da kuma rage parashen man petur.

Saidai a nan take, su ka yi watsi da wannan tayi.

Ya zuwa yanzu, mutane da dama su ka ji raunuka, a cikin wannan arangama, a yayi da jami´an tsaro su ka capke a ƙalla masu zanga-zanga 40.