1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Arangama tsakanin ƙungiyoyin ƙwadago da jami´an tsaro a ƙasar Guinee

January 17, 2007
https://p.dw.com/p/BuUE

A birnin Conakry na ƙasar Guinee, a na ci gaba da arangama, tsakanin jami´an tsaro da ƙungiyoyin ƙwadago.

A sakamakon taron gangamin da su ka shirya, ƙungiyoyin ƙwadago sun bukaci shugaban ƙasa, Lansana Konte, ya yi murabus daga muƙamin sa.

Shugaban Majalisar Dokoki ya kiri ƙungiyoyin su daina zanga-zanga, tare da alkawarta ƙarin albashi, da kuma rage parashen man petur.

Saidai a nan take, su ka yi watsi da wannan tayi.

Ya zuwa yanzu, mutane da dama su ka ji raunuka, a cikin wannan arangama, a yayi da jami´an tsaro su ka capke a ƙalla masu zanga-zanga 40.