Arangama a tsakanin tsagerun yakin sa kai a kasar Somalia
May 11, 2006Talla
Sojin sa kai na musulmai da kawancen madugan yaki a Somalia na ci gana da dauki ba dadi da juna, a kokarin da suke na kwace babban birnin kasar wato Magadishu.
Wannan dauki ba dadin dai na faruwa ne duk kuwa da yarjejeniyar tsagaitawa da bude wuta da aka cimma a tsakanin bangarorin biyu a jiya laraba.
Rahotanni da suka iso mana na nuni da cewa ya zuwa yanzu sojin sa kann musulmin na rike ne da kashi 80 cikin dari na birnin na Magadishu.
A dai dauki ba dadin daya faru a jiya laraba, an tabbatar da cewa mutane 13 ne suka rugamu gidan gaskiya, wasu kuma da dama suka jikkata.