Anyiwa prisononi afuwa a Burma | Labarai | DW | 03.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Anyiwa prisononi afuwa a Burma

Gwamnatin mulkin soji dake kasar Burma ta yiwa prosoni 2,800 afuwa,a bangaren bukin kewayowar ranar samun yancin kasar ,wadanda suka hadar wasu mutane 20,dake muradin ganin cewa an dawar da mulkin democradiyya a wannan kasa.Sai dai Tsararriyar mai fafutukan neman yancin democradiyya Aung San Suu Kyi,bata cikin wadanda akayiwa afuwan sai dai wadanda keda alaka da jammiyarta sun bayayana cewa ,akalla Prisononi masu fafutukan democradiyyan guda 27 aka yiwa afuwa,kuma tuni aka sake su.Jammiyyar National League ta San Suu kyi ce ta lashe zaben da aka gudanar a shekara tza 1990,sai dai sojoji wadanda ke mulkin kasar tun daga 1962,sunyi watsi da sakamakon zaben.Kawo yanzu dai gwamnatin sojin bata sanar da lokacin da zata samu yancinta ba.