Anyi tofin Allah tsine ga kisan gillar da akayiwa Bhutto | Labarai | DW | 27.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Anyi tofin Allah tsine ga kisan gillar da akayiwa Bhutto

Shugabannin Ƙasashen Duniya na ci gaba da tofin Allah tsine da kisan gillar da akayiwa Benazir Bhutto. Al´amarin a cewar da yawa daga cikinsu, abune da ka iya yin karan tsaye ga harkokin Dimokruɗiyya a ƙasar. Shugaba Bush ya bayyana harin da cewa, maƙiya mulkin Dimokruɗiyya da zaman lafiya ne a Pakistan keda hannu a cikinsa. Mr Bush ya kuma buƙaci Pakistan ci gaba da yaƙar ayyukan ta´addanci a ƙasar. Nan gaba ƙadan kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya zai gudanar da taro, don tattauna faruwar wannan al´amari. Kafin taron sai da majalisar tayi Allah wadai da waɗanda suka aikata wannan aiki. Itama ƙungiyyar Tarayyar Turai Eu, ta hannun shugabanta Jose Manuel Borroso, Allah wadai tayi da wannan kisan gilla da akayiwa Benazir Bhutto.