1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Anyi kira ga kasashen duniya da su kara maida hankali akan yaki da kanjamau

An gudanar da bikin ranar yaki da cutar kanjamau ta duniya tare da kira ga kasashen duniya da su kara mayarda hankali tare da ware kudade don yaki da cutar.

Rahotanni sunce kimanin mutane miliyan 40 ne suke dauke da kwayar cutar HIV wadda ke haddasa cutar ta kanjamau,rahotannin sunce ana sa ran kusan mutane miliyan 3 ne zasu mutu sakamakon cutar cikin wannan shekara.

Nahiyar Afrika dake dauke da kashi 10 cikin dari na yawan jamaar duniya ,itace keda fiye da rabin mutane da ke dauke da kwayar cutar HIV.

Kasar Senegal mai yawan musulmi itace kasa kadai da take da kashi daya cikin dari na jamaarta dauke da kwayar cutar.

A kasar India an kiyasta cewa mutane miliyan 5 da dubu dari daya suke dauke da kwayar cutar.

Haka dai labarin yake a sauran kashe musamman masu tasowa.