Anyi janaizar Raj Kumar | Labarai | DW | 13.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Anyi janaizar Raj Kumar

Mutane 4,da suka hadar da jamiin yansanda 1 ne suka rasa rayukansu a garin Bangalore dake kudancin India,alokacinda fada ya barke ,sakamakon hana mutane halartan janaizar wani sanannen tauraron yin film din india.Masu shaawar marigayi Raj Kumar kimanin sama da dubu 20 ne,suka tayar da bore,tare da farfasa motoci,domin samun sukunin shiga harabar filin wasanni ,inda aka ajiye gawarsa ,domin janaiza.Wannan rigingimu dai suncigaba da gudana,harya zuwa lokacin da aka dauki gawar mamacin ,domin binne shi a karkashin harabar filin wasan,inda yansanda sukayi ta harba barkonon tsohuwaSanannen dan film din India Raj Kumar mai shekaru 77 ya gamu da ajalinsa ne a jiyxa laraba,daga ciwon bugun zuciya.Shaguna da bankuna da kamfanoni sun kasance a rufe na tsawon kwanaki biyu,domin juyayin mutuwan Raj kumar,ayayinda aka sauke tutan India zuwa rabi a dukkan hukumomin gwamnati,domin nuna alhinin mutuwarsa.