Anyi garkuwa da turawa biyu kuma a Naija Delta | Labarai | DW | 23.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Anyi garkuwa da turawa biyu kuma a Naija Delta

A Najeriya tsageran yankin Naija delta sunyi awon gaba da wasu turawa biyu a birin Fatakwal a jerin sace sacen yan kasashen waje da suke ci gaba dayi a yankin.

Mai magana da yawun yan sanda ta jihar Rivers Barasua Ireju ta fadawa kanfanin dillancin labaru na AFP cewa an sace wadannan mutane biyu da sanyin safiyar yau talata cikin motarsu.

Hakazalika wani jamiin ofishin jakadancin Amurka a Lagos yace daya cikin mutanen dan kasar Amurka ne yayinda dayan kuma dan kasar Burtaniya ne.

Babu kuma kungiyar data fito ta dauki alhakin sace su.

A halinda ake ciki kuma mahukuntan kasar Philipines sunce yan kasarsu 24 yan bindiga sukayi awon gaba da su daga jirgin ruwa da suke ciki,tun farko jamian gwamnatin Najeriya sun sanarda cewa yan kasar Phillipine 6 ne aka sace.