Anyi garkuwa da Bajamushiya a Afghanistan | Labarai | DW | 19.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Anyi garkuwa da Bajamushiya a Afghanistan

Ma´aikatar harkokin wajen Jamus ta tabbatar da labarin garkuwa da akayi da wata bajamushiya, dake aikin bayar da agaji a kabul.Tuni dai ma´aikatar ta kafa wani kwamiti da zai duba wannan batu , domin ceto Bajamushiyar.Kungiyyar Taliban wacce tayi kaurin suna wajen yin garkuwa da yan ketare tace bata da hannu a cikin wannan al´amari.A wani labarin kuma mai magana da yawun kungiyyar ta Taliban yace ba a cimma wani abin azo a gani ba dangane da sauran yan KTK 19. A yanzu haka dai a cewar sa kungiyyar na tunanin mataki na gaba da zata dauka akan mutanen 19. Rahotanni dai sun nunar da cewa yan Taliban din na son gwamnatin Afghanistan sako mutanen tane da take tsare dasu, kafin su kuma su sako yan koriya ta kudun. To amma ya zuwa yanzu, gwamnatin ta Afghanistan taki ta mika wuya a game da wannan bukata.