Anyi dauki ba dadi da sojojin Majalisar dinkin duniya a Ivory Coast | Labarai | DW | 18.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Anyi dauki ba dadi da sojojin Majalisar dinkin duniya a Ivory Coast

A halinda ake ciki kuma tawagar sojojin Bangladesh na dakarun majalisar dinkin duniya dake Ivory Coast sun janye daga wani sansani dake yammacin kasar bayan wani dauki ba dadi da sukayi da magoya bayan shugaba Laurent Bagbo.

A kalla mutane hudu ne aka kashe sakamakon wani farmaki da aka kaiwa sansanin dakarun majalisar dinkin duniyar dake Guiglo wanda ke tazarar kilomita dari uku daga Abidjan.

A yau dai an shiga kwana na uku ke nan da magoya bayan shugaba Bagbon suke tada kayar baya dangane da kudurin masu shiga tsakani a rikicin kasar yan kasashen waje na rushe majalisar kasar wadda take cike da magoya bayan shugaban.

A dangane da hakanne kuma jamiyyar Mr Bagbon ta fice daga gwamnatin rikon kwaryar kasar da kuma tattaunawar sasantawa da majalisar dinkin duniya ke marawa baya, bugu da kari kuma gwamnatin ta umarci sojojin faransa da dakarun na majalisar dinkin duniya dasu fice daga kasar.