1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Antonio Guterres ya bayyana matsanacin halin rayuwa a Darfur

Shugaban kula da ‚yan gudun hijira na MDD Antonio Guterres yayi gargadin cewar yankin Darfur na fuskantar barazanar fadawa cikin mawuyacin hali na taimakon jinkai idan har ba’a gaggauta daukan tsauraran matakan tsaro da zai bada damar isar da taimakon kayayakin abinci ga masu bukata ba. Guterres yace yanzu hakan miliyoyin mutane na nan rai ga hannun Allah a yayinda daruruwa ke mutuwa sakamakon tsanannin yunwa, kana wasu na cigaba da rasa gidajen su. Gwamnatin Sudan ta yi watsi da tayin MDD na tsugunar da jami’an tsaron ta 20,000 a yankin na Darfur.