Annan yayi kira ga shugabannin Afirka da su rage kwadayin mulki | Labarai | DW | 10.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Annan yayi kira ga shugabannin Afirka da su rage kwadayin mulki

Babban sakataren MDD Kofi Annan yayi kira ga shugabannin kasashen Afirka da su girmama dokokin kasa kana kuma su guji daukar matakai na darewa kan mulki har abada. Annan ya bayana haka ne a cikin wata hira da jaridar Guardian mai zaman kanta ta yi da shi. Annan ya ce ya zama wajibi a amince da dokokin dake kunshe a kundin tsarin mulkin kasa. Wannan hira dai ta zo ne a daidai lokacin da ake kara yada jita-jita cewa shugaban Nijeriya Olusegun Obasanjo na neman yin tazarce bayan cikar wa´adin mulkinsa a badi idan Allah Ya kaimu. Annan ya ce bai kamata a canza kundin tsarin mulkin kasa ba don biyawa wasu bukatunsu don cimma burinsu na siyasa ba. Annan ya ce daukar irin wannan mataki ka iya jefa kasa cikin rudami da rashin zaman lafiya. Yanzu haka dai majalisar dokokin Nijeriya na tabka muhawwara akan shawarar da magoya bayan shugaba Obasanjo suka bayar na yiwa tsarin mulkin kasar kwaskwarima, don ba shi damar tsayawa takara a karo na uku.