Annan yayi kira da a kara daukar matakan rage yaduwar AIDS ko Sida | Labarai | DW | 02.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Annan yayi kira da a kara daukar matakan rage yaduwar AIDS ko Sida

Babban sakataren MDD Kofi Annan ya ce yanzu lokaci yayi da ya zama wajibi shugabannin kasashen duniya su cika alkawuran da suka dauka na rage yaduwar cutar AIDS ko Sida. A cikin wata sanarwa da ya bayar a ranar bikin AIDS ta Duniya da aka yi jiya alhamis, Annan ya ce dole ne a tashi a yi aiki tukuru don rage yaduwar cutar. Annan ya ce ko da yake duniya ta samu ci-gaba a yakin da ake yi da AIDS to amma har yanzu ba ta shawo kan yaduwar cutar ba. Alkalumma sun nunar da cewa mutanen da ke dauke da kwayoyin HIV mai haddasa cutar ta AIDS yanzu ya kai mutum miliyan 40.3 a duniya baki daya. Tun bayan bullar cutar a shekarar 1981 sama da mutane miliyan 20 suka mutu sakamakon kamuwa da ita.