Annan ya zargi Izraela da keta dokar sararin samaniyan Lebanon | Labarai | DW | 02.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Annan ya zargi Izraela da keta dokar sararin samaniyan Lebanon

Sakatare General na mdd Kofi Annan,ya zargi Izraela da cigaba da yin karan tsaye wajen samar da zaman lafiya tsakaninta da Lebanon,sakamakon cigaba da keta dokokin bin sararin samayan kann iyakokin kasashen biyu da jiragen ta keyi.Duk da wannan matsala,Jagoran mdd a wata wasika daya aikewa komitin sulhu a jiya,yace har yanzu ana darajawa yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a watan Augusta tsakanin Izraela da yan Hizbollahi,na Lebanon,kuma babu wani rikici daya sake kunno kasi.Sai dai Mr Annan yace dakarun kiyaye zaman lafiya dake sa ido a kann iyakokin kasashen biyu,sun ruwaito cewa Izraela ta keta dokar shawagi a sararin samaniyan yankin da jiragenta na yaki da motoci ta kasa.,wanda takeyi kusan kowane wayewan gari.Tuni dai Lebanon ta gabatar da kokenta dangane da wannan shawagi da dakarun izraelan ke cigaba dayi a kann iyakokin kasashen,duk da yarjejeniya da aka cimma.