1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Annan ya yi watsi da bukatun Amirka

Babban sakataren MDD Kofi Annan ya yi fatali da bukatun da Amirka ta gabatar cewar ka da a amince da kasafin kudin MDD na shekarun 2006 zuwa 2007 har sai an kammala yiwa gamaiyar ta kasa da kasa kwaskwarima. A lokacin da yake magana a birnin New York Annan ya ce ba haka ake gudanar da aiki a cikin Majalisar ta Dinkin Duniya ba. Annan ya ce muhimmin batun da ke gaban majalisar shine sauke nauyin dake kanta amma ba gudanar da sauye sauye ba. A cikin lokaci kankane Annan dai ya soke wata ziyarar makonni biyu da ya shirya kaiwa nahiyar Asiya saboda matsalolin kasafin kudin da MDD ke fuskanta. Majalisar na nuna damuwa cewar nan ba da dadewa ba zata kasa biyan albashin ma´aikatanta.