Annan ya yi kira ga ´yan jarida da su rika nuna basira | Labarai | DW | 10.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Annan ya yi kira ga ´yan jarida da su rika nuna basira

Babban sakataren MDD Kofi Annan ya yi Allah wadai da jaridun kasashen Turai da suka sake buga zane-zanen batanci ga Annabi Mohammed SAW. A lokacin da yake magana da manema labarai a birnin New York Mista Annan ya ce ko da yake yana goyon bayan ´yancin ´yan jarida, amma dole ne editoci na jaridu su rika nuna halin ya kamata da nuna basira a cikin aikin su. Sakatare janar din na MDD ya yi kuma suka ga tashe tashen hankulan da suka barke a lokacin zanga-zangar nuna adawa da zane-zanen. Annan ya ce bai kamata masu zanga-zangar su rika kaiwa wadanda ba su san hawa ba su san sauka ba hare hare na ba gaira ba dalili.