Annan ya yi kira ga musulmi da su yiwa jaridar Denmark gafara | Labarai | DW | 04.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Annan ya yi kira ga musulmi da su yiwa jaridar Denmark gafara

Babban sakataren MDD Kofi Annan yayi kira ga musulmi da su amince da gafara da wata jaridar Denmark ta nema game da fitinar da ta tayar bayan ta buga zane-zanen batanci ga Annabi Mohammad SAW. A cikin watan satumban shekara ta 2005 Jaridar Jyllands-Posten ta buga zane-zanen, amma ta nemi gafara a ranar litinin da ta gabata. Wasu jaridun kasashen Turai sun sake buga zane-zanen wadanda suka ta da hankalin musulmi a ko-ina cikin duniya, wanda ya janyo zanga-zangar nuna kyamar Denmark da kauracewa sayen kayayyakin kasar a kasashe da dama na yankin GTT. A jiya FM Denmark ya gana da jakadun kasashen musulmi dake kasar, inda ya nemi gafararsu.