1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Annan ya yi kira ga Falasdinawa da su fita kada kuri´a

Babban sakataren MDD Kofi Annan yayi kira ga Falasdinawa da su fita kwansu da kwarkwatansu don kada kuri´a a zaben ´yan majalisar dokokin da za´a yi a ranar laraba mai zuwa. A cikin wata sanarwa da ya bayar Annan ya ce zaben na matsayi wani muhimmin mataki a tarihin doguwar gwagwarmayar da al´umar Falasdinawa ke yi. Annan ya yi fatan cewa zaben zai bude hanyar samar da zaman lafiya mai dorewa a wannan yanki. Tun dai a jiya asabar jami´an tsaron Falasdinawa kimanin dubu 60 suka fara kada ta su kuri´ar, don ba su damar tabbatar da tsaro a lokacin zaben na ranar 25 ga watan nan na janeru.