1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Annan ya yi kira da a girmama addini da al´adu

February 3, 2006
https://p.dw.com/p/Bv9d
Babban sakataren MDD Kofi Annan ya fara wani kokari da nufin warware rigimar da ake yi sakamakon wasu zane-zane na Annabi Mohammad SAW da aka buga a wasu jaridun kasashen Turai. Mista Annan ya ce dole ne ´yancin fadan albarkacin baki ya girmama addini da al´adu. Annan ya ce kamata yayi a yi amfani da hanyoyin lumana tare da mutunta juna muddin ana son a warware rashin fahimta tsakanin addinai da al´adu. Don nuna fushin su dangane da wadannan zane zane kungyoyin masu kishin addinin Islama sun yi barazanar yin garkuwa da ´ya kasashen Turai. A Zirin Gaza wasu ´yan bindiga Falasdinawa sun farma ofishin KTT da ke wannan yanki. Yayin da a birnin Nablus wasu Falasdinawa suka sace wani malami Bajamushe, amma suka sake shi daga bisani.