1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Annan ya nuna damuwa game da rikicin Somalia

July 21, 2006
https://p.dw.com/p/Bupq
Babban sakataren MDD Kofi Annan ya nuna damuwa game da rahotannin da aka bayar cewa sojojin Habasha sun kutsa cikin Somalia. Masu aiko da rahotanni daga yankin sun ce sojojin Habasha sun shiga cikin birnin Baidowa don ba da kariya ga raunanniyar gwamnatin wucin gadin Somalia, wadda sojojin sa kai na Islama suka lashi takobin tumbuke ta. Wasu rahotanni da ba´a tabbatar da su ba sun rawaito wadanda suka shaida abin ya faru na cewa karin motocin yaki daga Habasha sun shiga birnin jiya da daddare. Rahotannin sun kara da cewa sojojin Habasha na son kafa wani yankin tsaro ne a birnin. To amma gwamnati a birnin Addis Ababa ta musanta cewa sojojinta sun kutsa cikin Somalia. A halin da ake ciki shugabannin ´yan Islama a birnin Mogadishu sun yi kira ga hadin kan kasar da kaddamar jihadi akan sojojin mamaye.