1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Annan a rikicin siyasar Kenya

Mohammed, ZainabFebruary 15, 2008

Kokarin warware rikicin madafan iko a Kenya

https://p.dw.com/p/D8FE
Tsohon Babban Sakataren Majalisar Ɗunkin Duniya,Kofi AnnanHoto: AP


A wannan makon ne ɓangarori biyu dake adawa da juna a ƙasar Kenya suka kusan cimma matsaya guda,sai dai har yanzu sun gaza cimma daidaito dangane da raba madafan iko,wanda shnie zai iya warware takaddamar siyasa data barke a wannan ƙasa,wanda ya haddasa asaran rayukan mutane sama da 1,000.

Kofi Annan ya faɗawa taron manema labaru a birnin Nairobin Kenyan cewa,suna daf da cimma warware wannan matsala,koda yake a yanzu ne suka isa mataki mai sarkakkiyyar gaske,acigaba da kokarin da yake yi na ganin cewa an gano bakin zaren kawo karshen rikicin siyasan na Kenya.

Tsohon jagoran Majalisar Ɗunkin Duniyan yana na kokarin ganin cewa an cimma daidaituwa tsakanin shugaba Mwai Kibaki da Jagoran 'yan adawa Raila Odinga,a wannan rikici dake da nasaba da sakamkon zaɓen shugaban ƙasa daya gudana a ranar 27 ga watan Disamban shekarar data gabata,rikicin da kori sama da mutane dubu 300 daga gidajen su.

An dai bayyana wannan rikici na siyasa da kasancewa mafi munin irinsa daya ritsa da wannan kasa dake zama zakaran tattalin arzikin ƙasashen dake yankin gabashin Afurka,da kasancewa mafi munin Irinsa tun daga samun 'yancin mulkin kana kasar a shekara ta 1963.

Annan yace an samu cigaba a wannan mako,wanda ya hadar da amincewa da nada komiti mai zaman kansa dazai sake nazarin zaɓen.

Ya kuma bayyana cewar ya na da matukar muhimmanci ɓangarorin biyu su amince da kafa gwamnatin haɗin kan kasa,wadda zata tabbatar da ganin cewa anyi gyaran kundun tsarin mulki da dokokin zabe a ƙasar ta Kenya .

Annan dai ya bayyana cewar zai sake ganawa da shugaba Mwai Kibaki da Shugaban Adawa Raila Odinga a ranar Litinin,ayayinda sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleeza ita ma zata kasance a Kenyan,domin taimakawa kokarin sa na sasanta bangarorin biyu,kafin koma teburin tattaunawa washe gari talata.


Duk da fatansu na ganin cewa rayuwa ta komo kamar yadda aka saba a baya,alummomin kasar ta Kenya sun fara nuna gajin hakuri da shugabannin nasu.Sai dai Kofi Annan ya bayyana musu cewar ba lallai bane tattaunawar warware irin wannan matsala ta cimma manufa cikin gaggawa kamar yadda ake muradi.Dole ne a tafi sannu a hankali domin cimma sakamako mai ɗorewa.

Odinga mai shekaru 63 da haihuwa na zargin Kibaki mai shekaru 76 da haihuwa da satan ƙuri'u.Kibaki dai yana ikirarin cewar shine mutumin daya lashe zaɓen na watan Disamba,tare da zargin 'yan adawn da ingiza rigingimu amaimakon kalubalantar sakamakon zaɓen a kotunan Shari'Aa