Ankashe masu zanga-zanga 50 a Kwango
September 20, 2016Talla
Rahotanni daga kasar Kwango na cewar adadin wadan da suka rasa rayukansu a wata arangama tsakanin 'yan adawa da jami'an tsaro ya haura 50, masu zanga-zanagar dai sun gudanar da gangamin ne a Kinshasha babban birnin kasar da nufin matsa wa shugaba Josesp Kabila lamba domin a bayyana jadawalin gudanar da zabubuka a kasar.
Gamaiyyar jam'iyyun adawa a kasar Kwango, sun yi magoya bayansu da su fito dan ci gaba da fafutuka na nuna kin jinin gwamnatin shugaba Joseph Kabila wanda wa'adin mulkinsa ke shirin kawo karshe. A shekara ta 2001 ne dai shugaba Joseph Kabila ya dare karagar mulkin kasar Kwango wanda yanzu ya ke nuna alamun neman wa'adi na biyu.