Angela Merkel za ta sake yin takara a zaben 2017 | Siyasa | DW | 20.11.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Angela Merkel za ta sake yin takara a zaben 2017

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayyana wa manyan jiga-jigai na jam'iyyarta ta CDU cewar za ta sake tsayawa takarar neman shugabancin gwamnatin Jamus a shekara mai zuwa a karo na hudu.

Wannan dai sanarwa  ta kawo karshen rade-radi na cewar ko Merkel da ke zama mace mai karfin fada a ji a duniya za ta sake tsayawa takarar.Duk da sukar da wasu masu zabe a kasar ta Jamus suka yi kan tsarin shugabar gwamnatin  na 'yan gudun hijira, ana kallon shugabar gwamnatin a matsayin wata jigo a cikin EU.Kungiyar ta EU ta girgiza dai bayan ficewar Birtaniya daga cikinta yayin da a bangaren guda aka zabi Donald Trump a matsayin shugaban Amirka mai jiran gado.Shugabar gwamnati Angela Merklel dai ta bayyana haka ne bayan tattaunawa da mambobin jam'iyyarta ta CDU a birnin Berlin. Abin da ke share fage na taron jam'iyyar a watan Disamba da ke tafe.