1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Angela Merkel tace akwai bukatar fadada samarda makamashi

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel tace katsewar harkokin jigilar man fetur daga Rasha ya nuna bukatar dake akwai ta kara fadada aiyukan makamashi na kasar.

Shugabar ta Jamus tace gwamnatin Jamus tana bukatar sake duba illar dake tattare da shirin da take da shi na soke batun makamashin nukiliya.

Merkel ta fadi haka ne saoi kadan bayan da Rasha ta katse aikewa da man fetur ta bututun Druzhba .

Gwamantin Rasha tace kasar Belarus tana karkata akalar bututun man fetur ba tare da izni ba ta hanyar bututun mai daya ratsa cikin iyakokinta.

Bututun man na Druzhba shike samarda kashi 20 cikin dari na mai da Jamus take shigo dashi a kowace shekara.