Angela Merkel ta yi kira da a ƙara matsawa Iran lamba | Labarai | DW | 26.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Angela Merkel ta yi kira da a ƙara matsawa Iran lamba

SGJ Angela Merkel ta ce Jamus zata goyi da bayan duk wani mataki na tsananta takunkumi akan Iran face kasar ta amince ta dakatar shirin ta na nukiliya. A jawabin ta na farko ga babban taron MDD SG ta Jamus ta yi kashedin cewa idan aka kyale Iran ta malakai makaman nukiliya to haka zai haddasa mummunan sakamako.

Merkel ta ce: ”Bai kamata kan gamaiyar kasa da kasa ya rarrabu wajen daukar mataki na bai daya kan Iran ba. Ba duniya ce zata ba wa Iran shaidar cewa ka da ta kera makaman nukiliya ba, a´a Iran din ce ya zama dole ta nunawa duniya cewa ba ta bukatar makaman nukiliya.”

Merkel ta kuma yi amfani da jawabinta wajen nuna bukatar Jamus ta samun kujerar dindindin a kwamitin sulhu tana mai cewa yadda tsarin kwamitin ya ke a yanzu bai dace da wannan zamani da duniya ke ciki ba. Ta kuma yi kira ga shugabannin duniya da su amince su dauki karin tsauraran matakai na yaki da dumamar doron kasa.