1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Angela Merkel ta isa birnin Tel Aviv a Isra´ila

January 29, 2006
https://p.dw.com/p/BvAJ
Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta sauka a Isra´ila a rangadin ta na farko zuwa yankin GTT tun bayan darewarta kan mulki watanni biyu da suka wuce. A wani lokaci da yammacin yau zata gana da FM rikon kwarya Ehud Olmert a birnin Kudus. Sannan a gobe litimnin zata tashi zuwa birni Ramallah inda zata gana da shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas. Ana sa rai tattaunawar da Merkel zata yi da shugabannin yankin zata fi mayar da hankali ne akan halin da ake ciki a yankunan Falasdinawa bayan zaben makon jiya sai kuma batun shirin nukiliyar Iran. A kuma halin da ake ciki Merkel ta yi fatali da bukatar da kungiyar Hamas ta gabatar na ganawa da shugabannin kungiyar, wadda ta lashe zaben ´yan majalisar dokokin Falasdinawa da aka gudanar a ranar laraba.