Angela Merkel ta gargadi baki a jamus | Labarai | DW | 26.09.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Angela Merkel ta gargadi baki a jamus

shugabar gwamnatin Jamus ta yi kira ga baki 'yan ci rani da ke zaune a Jamus da su yi kokarin sajewa da al'umar kasar ta hanyar koyon yare

default

Angela Merkel

Shugabar Gwamnatin kasar Jamus Angela Merkel ta yi gargadi ga baki 'yan ci rani da su yi kokarin sajewa da al'umar kasar ta hanyar koyon yaren  tare kuma da muntunta dokokin kasar. 

Merkel wacce ta ke magana a wajan taron congres na jam'iyyar CDU a Mayance wanda ke a yammacin kasar ta jamus.

Ta ce ya zama wajibi ga mai sha'awar zama a kasarmu ya kasance ya  na mai bi kaidojin da suka dace na kundn tsarin mulkin, sanan kuma ta yi gargadi daidaita hakin mata tare da daina nuna masu waria a kan dukanin al amuran rayuwa na yau da gobe .

Wannan sanarwa dai da shugabar gwamnatin ta jamus ta bayyana ta zone a lokaci da masu yin sharhi akan al 'amuran y siyasa  ke nuna cewa kwarjini shugabar ya zube yau kusan shekara guda tun bayan zabubukan da aka gudanar a kasar.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane

Edita        : yahouza sadissou Madobi